Kasar China za ta aiwatar da sabbin matakai saboda karuwar sabbin nau'in kwayar cutar Coronavirus (Kovid-19) a yankin Jiangching da ke lardin Yunnan, wanda ke kan iyaka da Myanmar.
Gwamnatin kasar China ta sanar da cewa, za a rufe makarantu da kasuwanni daga 26 zuwa 27 ga watan Yulin a yankin Jiangchang, kudu maso gabashin birnin Pu'er, kuma za a hana shiga da fita a yankin.
Saboda karuwar yawan mutanen da suka kamu da kwayar cutar a Jiangching, an tsaurara matakan.
Mahukunta sun bayar da rahoton cewa za a yi wa duk mazauna yankin gwajin Kovid-19.
A lardin Yunnan, akwai marasa lafiya 297 wadanda 218 daga cikinsu sun fito daga ƙasashen waje, ana ci gaba da kula da su.