China za ta kara aikawa Serbia da allurar riga-kafin Korona

China za ta kara aikawa Serbia da allurar riga-kafin Korona

Kasar China ta bayyana za ta aikawa kasar Serbia da karin allurar riga-kafin Korona dubu 500,000 sanfarin Sinopharm a watan Maris.

Kamar yadda kafafen yada labaran suka rawaito an kammala shirye-shiryen aikawa da allurar riga-kafin wanda aka yi tsakanin shugaban Xi Jinping da takwaransa na Serbian Aleksandar Vucic. An shirya kai allurar riga-kafin a ranar 5 ga watan Maris wanda yazo daidai da ranar zagayowar haihuwar Vucic shugaban kasar Serbia.

Kasar Serbia ta karbi allurar riga-kafin Korona dubu 500,000 daga kasar China a farkon watan Febrairu bayan Beijin ta aika da kwara miliyan daya a kasashen Balkan.


News Source:   ()