Kasar China ta yanke shawarar tsawaita takunkuman kan iyakokinta da ta sanya saboda kwayar cutar corona (Covid-19) har zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.
A cewar labaran Wall Street Journal, jami'an kiwon lafiya na kasar China sun yanke shawarar ne saboda sabbin salon Covid-19 da aka gano a kasar.
Yayin da aka gano sabbin mutane 25 a cikin awanni 24 dauke da sabon salon Covid-19 a kasar China, adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa dubu 91 da 629.
A kasar mutane 4,636 ne suka mutu tun farkon annobar har izuwa yau.
A gefe guda kuma, China ta zama kasar da ta fi yawan alluran riga-kafin Covid-19 tare da allurai biliyan dubu 1 da miliyan 50.