China ta sake harba tauraron dan adam don sanya idanu a tekun Maliya

China ta sake harba tauraron dan adam don sanya idanu a tekun Maliya

China ta sake harba tauraron dan adam a karo na 3 don sanya idanu a tekun Maliya.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewar an harba tauraron dan adam na Hay Yang-2C da kumbon Long March-4B a cibiyar harba taurarun dan adam ta Chiuchuen da ke arewa maso-yammacin kasar.

Tauraron HY-2C da Hukumar Kimiyyar Sararin Samaniya ta China ta samar zai yi aiki tare da taurarun HY-2A da HY-2B da aka harba a baya.

A makon da ya gabata ma China ta harba taurarun dan adam guda 9 zuwa sararin samaniya.


 


News Source:   ()