Kutsen da aka yi wa Amurka ya faru a watan Disambar da muke ciki wanda ya bai wa masu kutsen damar shiga wasu sassa dake kula da harkokin kuɗi na ƙasar kamar yadda wata wasika da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani ta nuna.
A ranar talata ne Beijin ta yi martani kan zargin da Amurka ta yi mata cewar ta ɗauki nauyin kutse na internet a sashin kula da asusun kuɗinta.
A cewar sashin kula da asusun kuɗin na Amurka kutsen ya faru a farkon wannan wata lokacin da masu datsar bayanai suka kutsa tare da ganin wasu takaddu da basa ɗauke da muhimman bayanai.
Sai dai ƙasar China ta musanta bayanan ta hannun ma’aikatar kula da harkokin waje inda ta ce Beijin ba ta goyan bayan duk wani aiki na kutse ta internet kuma kwata-kwata bata goyan bayan yaɗa bayanan ƙarya saboda dalilai na siyasa kan China.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI