China ta kasance kasa ta uku da ta fara aika na'ura duniyar Mars

China ta kasance kasa ta uku da ta fara aika na'ura duniyar Mars

Na'urar da China ta samar mai suna Zhurong da zummar yin bincike a duniya Mars ya sauka akan jan planet din.

Kamar yadda Hukumar Harkokin Sararin Samaniyya ta sanar (CNSA) na'urar ya yi nasarar sauka samun lafiya a saman duniya Mars.

An sanar da cewa Zhurong ya sauka a kan wani lawa a kudancin Mars da aka gano a baya.

Baya ga Amurka da Rasha, China ta kasance kasa ta uku da ta fara aika na'ura zuwa duniyar Mars.

Na'urar wanda aka sanya wa suna Zhurong, mai nufin allan wuta da yaƙi a cikin tatsuniyoyin Sinawa, ya tashi a watan Yulin shekarar 2020 kuma ya isa duniyar Mars a cikin watanni 7, wanda ya ɗauki watanni 3 kafin ya fara tafiya a tarafkin sararin samaniya.

 


News Source:   ()