Kasar China ta aika da tauraron dan adam da mutum mutumin tauraron dan adam da zasu yi aiki domin bincike akan duniya Mars zuwa sararin samaniyya.
Dangane ga bayanan da suka fito daga kanfanin dillancin labaran China mai suna Xinhua , tauraron da akan radawa suna "Tianwen-1" wanda zai yi aikia a duniyar Mars da kuma Long March-5 an aikasu zuwa sararin samaniya.
Tauraron dan adam din da mutum mutumin sararin samaniyya da aka harba daga tsibirin Hainan dake kudu maso yammacin kasar sun isa yankin da ake so bayan mintuna 45 da harba su.
Ana hasahsen cewa zasu isa yankin da zasu yi aikin da ake so bayan watanni bakwai.