China ta fitar da sabbin matakan inganta tattalin arziki saboda nasarar Trump

China ta fitar da sabbin matakan inganta tattalin arziki saboda nasarar Trump

Kasar na shirin kawo karshen basussukan biliyoyin daloli domin tunkarar kalubalen da ke neman zame mata karfen kafa.

Trump ya yi alkawarin kara harajin shigo da kaya, ciki har da harajin da ya kai kashi 60 cikin 100 kan kayayyakin da China ke kerawa.

Nasarar da ya samu a yanzu na iya kawo cikas ga shirin Xi Jinping na mayar da kasar mai karfin fasaha da kuma kara yin tsamin dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu masu karfin tattalin arziki a duniya.

A wa'adin mulkinsa na farko Trump ya dorawa kayayyakin China harajin da ya kai kashi 25%.

Wani manazarci a China mai suna Bill Bishop ya ce kamata ya yi a dauki maganar Trump game da sabon shirinsa na haraji da muhimmanci.

Tun kafin nasarar zaben Trump da kuma bayan China ta fara fitar da matakan tallafawa tattalin arzikinta a watan Satumba, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya rage hasashe sa game da burin ci gaban kasar a kowace shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)