Jirgin balaguron Zhang-5 na kasar China ya bar Wata don kawo samfurin ƙasa da burbuɗin da ya tattara a cikin watan zuwa Duniya.
Kanfanin dillancin labaran Xinhua, Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Kasar China ta (CNSA) ta sanar da cewa, jirgin binciken "Zhang-5" ya taso daga cikin wata don kawo samfurin kasa da ya tattara zuwa Duniya.
An yi hasashen cewa burbudin da Zhang-5 ya tattara za su iya taimakawa wajen haske da kuma bayar da gudumuwa ga nazarin sararin samaniya.
Idan har aka kammala aikin, wanda aka tsara zai dauki kwanaki 23, China zata zama kasa ta uku bayan Amurka da Tarayyar Soviet da suka kawo burdudi daga Wata zuwa Duniya.