A ranar Asabar da ta gabata ne dai shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da ɗaukar tsauraran matakai kan manyan abokan hulɗar kasuwancinsu irinsu Canada da kuma Mexico, tare da ƙara wa kayayyakin China harajin kashi 10.
To sai dai ƴan kwanaki kaɗan bayan faruwar hakan, Beijin ta sanar da ƙarin kashi 15 kan makashin da Amurka ke kai wa ƙasarta, da kuma ƙarin kashi 10 kan kayayyakin noma da manyan motoci da kuma na ɗaukar kaya.
Ta ce ta ɗauki matakin ne don mai da martani kan ƙarin harajin da Washinton ta yi mata.
China ta ce matakin na Amurka ya saɓa wa dokar Hukumar Kasuwanci ta Duniya, kuma hakan ba zai magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ba face ƙara dagula lamuran kasuwanci tsakanin China da Amurka.
Ita dai China ta kasan ce babbar kasuwar da Amurka ke sai da makamashinta, domin a wasu alkaluma da Hukumar Hana Fasa Kwauri ta ƙasar ta fitar, sun nuna cewa Amurka ta kai makamashin kwal da kuma isgar Gas na sama da Dala biliyan 7 a shekarar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI