China: Ficewar Amurka daga Afghanistan wa ta dama ce

China: Ficewar Amurka daga Afghanistan wa ta dama ce

China ta yi maraba da ficewar sojojin Amurka da na NATO daga Afghanistan inda ta kara da cewa ya ba da wata sabuwar dama ga jama'ar Afghanistan.

Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ya ce "Tare da ficewar Amurka da NATO daga yankin, jama'ar Afghanistan sun samu wata sabuwar dama ta yin la’akari da makomar kasar" 

Vang ya kuma yi kira ga kungiyar Taliban, wacce ta sake karfafa ikonta a yankin, da ta katse duk wata alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

A gefe guda kuma, Vang ya jaddada cewa Amurka, wacce sojojinta suka kasance a kasar na shekaru 20, lamarin da bai samar da mafita ba, ya kamata ta yi zurfin tunani game da rawar da take takawa a Afghanistan.


News Source:   ()