Wannan nasara ta biyo bayan bajintar da 'yan wasan China suka yi a gasar harbi da bindiga na maza da mata da kuma ninkayar mata.
Ita kuwa Australia ta samu nata zinaren ne a gasar tseren keke na mata da akayi yau asabar.
Yuting Huang da Lihao Sheng suka lashe zinare a gasar harbi mai nisan mita 10 da aka kammala yau da safe, bayan doke tawagar 'yan wasan Koriya ta Kudu, Jihyeon Keum da Hajun Park wadanda suka lashe azurfar gasar, sai kuma Islam Satpayev da Alexandra Le na kasar Kazakhstan da suka lashe tagulla.
China ta sake lashe zinare a gasar tsalle tsalle wadda Yani Chang da Yiwen Chen suka yi, sai kuma Amurka da ta samu azurfa ta hannunKassidy Cook da Sarah Bacon, sannan Birtaniya da at samu tagulla ta hannun Scarlett Mew Jensen da Yasmin Harper.
A gasar tseren keke kuwa, Grace Brown ta Australia lashe zinare, yayin da Anna Henderson ta Birtaniya ta samu azurfa, sai kuma Chloe Dygert ta Amurka da ta samu tagulla.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI