Kanfanin wutar lantarki na kasar Ingila mai suna Centrica ya sanar da cewa zai kori ma'aikata dubu biyar daga aiki.
Dangane da bayanan da suka fito daga kanfanin mai hidimar gas da wutar lantarki a Birtaniya watau Centrica domin kare kanfanin daga rushewa an yanke hukuncin dakatar da ma'aikata dubu 5 daga aiki.
Sanarwar ta kara da cewa korar aikin nada nasaba ga hasarar da kanfanin ya yi a shekarar 2019 da kuma faduwar farashin iskar gas.
Wani babban jami'ain kanfanin mai suna Chris O'Shea ya bayyana cewa fiye da rabin wadanda kanfanin zata kora daga aiki wadanda ke aikin kula da ma'aikata ne.
Kanfanin Centrica, nada ma'aikata dubu 27.