Daraktan Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka (CDC) Robert Redfield ya bayyana cewar takunkumin fuska ya fi allurar riga-kafi bayar da kariya daga Corona (Covid-19).
Darakta Redfield ya halarci wani zama da aka yi a Zauren Majalisar Dokokin Amurka inda ya bayar da bayanai game da matakin da ake a kan wajen yaki da Corona a kasar.
Redfield ya ce, har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa a Amurka, kuma ko an samo allurar riga-kafin cutar, ba za ta tafi a lokaci guda ba, hanyoyin kula da taka tsan-tsan na da matukar muhimmanci.
Redfield ya yi nuni da irin muhimmancin da takunkumin fuska ke da shi inda ya ce
"Akwai aiyukan kimiyya da suka tabbatar da irin rawar da takunkumin fuska yake bayarwa wajen hana kamuwa da cutar, har ma zan iya cewa, takunkumin rufe fuska ya fi allurar riga-kafi bayar da garanti game da samun kariya daga cutar."
Redfield ya ci gaba da cewar allurar riga-kafi ba lallai ne ta yi wa kowa aiki ba, amma takunkumi zai yi amfani ga duk wanda ya saka shi yadda ya kamata.