Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya tattaunawa da takwaransa na Afghanistan Hanif Atmar ta wayar tarho.
Kamar yadda kafafen diflomasiyyar kasar Turkiyya suka rawaito a tattaunawar an tabo batun samar da lumana a kasar Afghanistan.
Haka kuma Cavusoglu ya bayyanawa Amtar irin matakan Turkiyya da kuma shirin da ake yi bayan taron kolin NATO da aka gudanar a ranar 14 ga watan Afirilu.
Turkiyya na hadaka da Majalisar Dinkin Duniya da Katar akan lamarin samar da lumana a kasar Afghanistan.