Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya tattauna ta wayar tarho da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg.
Dangane da bayanan da aka samo daga majiyoyin diflomasiyya, a tattaunawar Cavusoglu da Stoltenberg an tabo shirye-shiryen taron kolin NATO da za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuni.
Haka kuma sun tattauna akan shirye-shiryen NATO na shekaru goma nan zuwa gaba wanda aka shirya kaddamarwa a shekarar 2030 da kuma lamurran kasar Afghanistan.