Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya tattauna da sakatare janar na NATO Jens Stoltenberg inda suka tabo batun yankin Libiya.
Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito Cavusoglu da Stoltenberg sun tattauna ta wayar tarho.
An nuna cewa an gudanar da taron ne gabanin taron kolin NATO da za a gudanar a ranakun 23-24 ga watan Maris a Burussel babban birnin kasar Beljiyom.
A taron baya ga muhimman abubuwa da suka shafi yankin an kuma tabo lamurran yankin Libiya.