Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya tattauna ta wayar tarho da Wakilin Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya a Libiya dan kasar Slovakiya Jan Kubis.
Majiyoyin diplomasiyya sun bayyana cewar, Cavusoglu ya taya Kubis murnar sabon aikin da aka ba shi.
Sakamakon dalilan rashin lafiya a watan Maris din 2020 Wakilin MDD a Libiya Gassan Selame ya yi murabus daga aikin da ya ke yi tun 2017.
A baya Jan Kubis ya yi aikin Mai Kula da sha'anin MDD a Libiya da kuma Wakilin Majalisar na Musamman a Iraki.