Ministan Harkokin Wajen Mevlut Cavusoglu ya gana da firaiministan rikon kwarya na Haiti kuma Ministan Harkokin Wajen kasar Claude Joseph.
A cewar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Turkiyya ta fitar, Cavusoglu ya tattauna ta wayar tarho da firaiministan rikon kwarya da Ministan Harkokin Wajen Haiti Joseph.
A yayin ganawar, minista Cavusoglu ya isar da ta'aziyyarsa akan rashin shugaban Haiti, Jovenel Moise, wanda ya rasa ransa a kisan da aka yi masa a gidansa, ya kuma jaddada cewa Turkiyya a shirye take ta taimakawa kasar.