Ministan Harkokin Waje na Turkiyya, Mevlut Cavusoglu ya karbi bakuncin Emine Ceppar, Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Yukren.
Cavusoglu wanda ya fitar da sanarwa a shafinsa na Twitter ya bayyana cewar ya karbi bakuncin Ceppar a karon farko a wannan mukaminsa kuma sun tattauna kan alakar kasashen biyu da kuma batutuwan yankin a taron.
Cavusoglu ya bayyana cewar "A matsayinmu na masu azamar kare Crimea, a koyaushe muna tare da 'yan Tatar na Crimea."
Ministocin Cavusoglu ya jawo hankali ga goyon bayan da Yukren ke ba wa yankin Azabaijan kuma ya kara da cewa Turkiyya ta yaba yunkurin.