Cavusoglu ya jajantawa Atmar

Cavusoglu ya jajantawa Atmar

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya jajantawa takwarasa na Afganistan Hanif Atmar da ya samu lafiya bayan kamuwa da cutar Corona.

Sanarwar da Cavusoglu ya fitar ta shafin Twittwr ta ce,

"Ina farin ciki da yadda ka samu lafiya baki daya. Ina fatan za mu gana nan da wani dan lokaci don tattauan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi yankunanmu da jama'armu."

Atmar ya sanar da cewa, ya warke daga cutar Corona, kuma ya godewa likitoci da ma'aikatan lafiya na Turkiyya.

 


News Source:   ()