Cavusoglu: "Dole a kama wadanda suka kai hari kan Masallacinmu a Jamus"

Cavusoglu: "Dole a kama wadanda suka kai hari kan Masallacinmu a Jamus"

Ministan Harkokin Waje na Turkiyya, Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewar harin da aka kai kan wani Masallaci kusa da birnin Stuttgart da ke Jamus ta hanyar rataye kan alade a kofar, shi ne misalin karshe na wariyar launin fata da nuna kiyayya ga Addinin Musulunci a Turai kuma ya kamata a kama wadanda suka aikata aikin kai tsaye.

Cavusoglu, a sakon da ya yada a shafinsa na Twitter ya ce,

"Ko da yake ana cikin watan Ramadhana mai girma da annobar da ake fama da ita, wariyar launin fata da nuna kiyayya ga Addinin Musulunci ya ci gaba a Turai. Mummunan harin da aka kai kan Masallacinmu a Jamus shi ne misalin karshe na wannan. Alamar da aka yi amfani da ita a cikin wannan mummunan lamari ya nuna rashin tunani. Tilas ne a kama wadanda suka aikata wannan lamarin kai tsaye.

An rataye kan alade a kofar Masallacin Fatih, wanda ke da alaƙa da Kungiyar Hadin Kan Addinai ta Turkiyya (DITIB) da ke garin Vaihingen Enz, kusa da Stuttgart a Jamus da misalin karfe 11:30 na dare.

An dauki bidiyon harin da aka kai kan Masallacin da kyamarorin tsaro, kuma an bayyana cewar an ga mutane biyu suna gudu daga wurin da sauri.


News Source:   www.trt.net.tr