Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya yi kira da a dauki matakan kauda kalubalanta da cin zarafin ýan gudun hijira a doron kasa.
Mevlut Cavusoglu ya yada wata sako a Twitter game da ranar yan gudun hijira inda yake cewa,
A Turkiyya akwai miliyoyin ýan gudun hijira da aka baiwa mafaka akan haka muke masu murnar ranar yan gudun hijira tare da kira da a dauki matakan dakile kalaman kiyayya da ake yi akan yan gudun hijira.
Cavusoglu ya kuma yada wani faifan bidiyon jawabin shugaba Recep Tayyip Erdogan da ya yi a zauren Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya akan ýan gudun hijira.