Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu ya tattauna da takwaransa na Azabaijan, Ceyhun Bayramov kan halin da ake ciki a Nagorno-Karabakh.
A sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Azabaijan ta fitar an bayyana cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu da takwaransa na Azabaijan, Ceyhun Bayramov sun tattauna ta wayar tarho.
Cavusoglu da Bayramov sun yi musayar ra'ayi game da sabon halin da ake ciki a Nagorno-Karabakh.
Ministocin sun jaddada muhimmancin 'yantar da yankunan Azabaijan daga mamaya domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin.
Bayramov ya tattauna da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov a Moscow, babban birnin Rasha a jiya, inda suka tattauna kan ci gaban da aka samu a Nagorno-Karabakh.