Canjin yanayi matsala ce da ke bukatar kulawar gaggawa

Canjin yanayi matsala ce da ke bukatar kulawar gaggawa

An ƙaddara cewa kashi 64 cikin 100 na yawan mutanen duniya suna ganin canjin yanayi a matsayin wata matsala da ke bukatar kulawar gaggawa a duniya.

Shirin Raya Kasa na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ya buga sakamakon binciken yanayi wanda mutane miliyan 1.2 daga kasashe 50 suka shiga ciki.

Dangane da sakamakon wannan binciken, mafi girma na ra'ayoyin jama'a da aka taba gudanarwa kan sauyin yanayi, kaso biyu cikin uku (kashi 64 cikin 100) na yawan mutanen duniya na ganin canjin yanayi a matsayin wata matsalar gaggawa ta duniya kuma suna son a dauki mataki.

A cikin kasashen da mai da iskar gas sune tushen fitar da hayaki, masu bada ra’ayoyinsu sun tallafawa amfani da makamashi mai sabuntawa, yayin da wasu manyan matakai na yaki da canjin yanayi sun hada da kare gandun daji da aikin gona mara illa ga yanayi.


News Source:   ()