Tun a shekarar da ta gabata ne dai dangantaka ta yi tsamine tsakanin ƙasashen India da kuma Canada, bayan da fara ministan Canada Justin Trudeau ya ce yana da hujjojin da ke tabbatar da cewar jami’an India ne suka kashe jagoran ƴan awaren Sikh a cikin ƙasarsu.
Ma’aikatar kula da harkokin ƙasashen wajen Canada ta ce, ta ɗauki matakin ƙorar jami’an ne, bayan da kwararan hujjoji suka tabbatar da hannunsu game da kisan Nijjar.
Ta ce ta buƙaci India da ta janye rigar ƙariyar da jami’an ke da ita, don baiwa hukumomin ƙasar bamar bincikarsu game da wancan zargi, amma sai dai taki yin hakan.
A nata martanin, ma’aikatar kula da harkokin wajen India, ta ce ta janye jami’an ta ne daga Canada, sabida rashin tabbacin tsaron lafiyarsu daga hukumomin Canadan.
Ma’aikatar ta kuma ce, ta umarci 6 daga cikin jami’an difulomasiyar Canada da su fice daga ƙasar nan da ranar Asabar mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI