Ƙasashen Brazil da Rasha da India da China ne suka kafa Kungiyar a shekarar 2009, inda a 2010 aka saka Afirka ta Kudu a ciki, inda ake ganin an kafa ta domin gogayya da ƙasashe bakwai mafi ƙarfin tattalin arziƙi.
A bara ne ƙasashen suka tsunduma ƙasashen Iran da Masar da Habasha da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa a cikin ƙungiyar.
Sannan kuma ƙungiyar ta gayyaci Saudiyya domin ta shige ta. Sai kuma Ƙasashen Turkiyya da Azerbaijan da Malaysia a hukumance da suka aika da buƙatarsu ta zama mambobi,
Nijeriya ce ƙasa ta tara da ta zama abokiyar hulɗar BRICS bayan Belarus da Bolivia da Cuba da Kazakhstan da Malaysia da Thailand da Uganda da kuma Uzbekistan.
Sai dai ƙasashen sun sanar da aniyarsu ta fitar da sabuwar hanyar biyan kuɗi ba tare da dogara da dalar Amurka ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI