Lula da Silva na ganin akwai buƙatar ƙasashe su sanya a ransu cewa dole kawar da matsalar ɗumamar yanayin cikin gaggawa don zaman lafiyar duniya, lura da illar da tuni duniya ta fara gani kama daga bala’o’i masu alaƙa da ambaliyar ruwa ko aman wutar dutse ƙarancin zubar ruwan sama tsananin zafi da sauran ibtila’in da ake gani a sassa daban-daban.
Yayin jawabin nasa shugaba Lula wanda ƙasar shi ta karɓi baƙoncin taron na G20 da aka shafe kwanaki biyu ana yi, ya bayyana cewa ya zama wajibi a yi gaggawar kawo ƙarshen illar fitar da tiriri mai guba da ƙasashe ke yi don tseratar da muhalli nan da shekarar 2040 zuwa 2045 tun kafin shekarar 2050 da aka sanya bisa ƙa’ida za a kawar da matsalar.
Lula wanda ke wannan batu a wani yanayi da ake fargabar yiwuwar zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya janye ƙasar, daga duk wata yarjejeniyar yanayi da ake ganin matakin ya iya ta’azzara barazanar dumamar yanayin da duniya ke fuskanta, sai dai shugaban na Brazil ya ce matakan da ƙasashe ke ɗauka wajen tunkarar matsalar ya kasa dole zai an ƙara ƙarfi.
Kasashe da dama dai na tafiyar hawainiya wajen aiwatar da manufofin yaƙar matsalar ta ɗumamar yanayi wadda masana ke ganin lokaci na gab da ƙurewa duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI