Borrell ya bukaci kawo karshen fuska biyu dangane da sammacin kama Netanyahu

Borrell ya bukaci kawo karshen fuska biyu dangane da sammacin kama Netanyahu

Borrell ya shaida wa taron ministocin kungiyar dake gudana a Italia cewar ya zama wajibi kasashen 7 su goyi bayan ICC wajen kama wadannan shugabannin da zaran sun shiga kasashen su kamar yadda doka ta tanada.

Jami’in yace lokacin da kotun ICC ta bada irin wannan sammaci a kan shugaban Rasha Vladimir Putin, kasashen na G7 da nahiyar Turai gaba daya sun yi murna da matakin, amma yanzu kuma wasu daga cikin su na jan kafa da kotun ta nemi Netanyahu da ministansa.

Borrell yace idan Amurka wadda bata rattaba hannu wajen amincewa da matsayin kotun ICC ta ki aiwatar da umarnin ta ba, ana iya fahimtar matsayinta, amma su kasashen G7 da na Turai da suka sanya hannu a kai basu da hurumin kin aiwatar da umarnin kama shugabannin.

Babban jami’in diflomasiyar ya shaidawa ministocin kungiyar G7 dake taro a Italia cewar ya zama wajibi su goyi bayan ICC domin karfafa ta da kuma tabbatar da cewar ana amfani da dokokin duniya a koda yaushe akan duk wanda ya taka doka.

Borrell ya kuma ce har yanzu Israila na amfani da yunwa wajen azabtar da Falasdinawan dake Gaza wajen hana kai musu kayan agaji.

Jami’in yace ya zama dole a fito a fadawa duniya gaskiyar lamarin abubuwan dake faruwa da kuma bukatar ganin Isra’ilar ta amince da shirin tsagaita wutar da aka gabatar mata ba tare da bata lokaci ba, domin kawo karshen kasha kashen dake gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)