Borrell ya buƙaci EU ta lafta takunkumi kan ministocin Isra'ila

Borrell ya buƙaci EU ta lafta takunkumi kan ministocin Isra'ila

Borrell ya ce, kalaman na kiyayya da ministocin ke furta su kan Falasɗinawa sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, yana mai cewa, lallai ƙasashen na Turai za su iya yanke shawarar sanya takunkuman muddin suna buƙatar haka.

Kodayake mista Borrell bai ambaci sunan koda mutum guda ba daga cikin ministocin na Isra’ila, amma a makwannin da suka gabata, ya caccaki ministan tsaron ƙasar, Itamar Ben-Gvir da kuma ministan kuɗi Bezalel Smotritch a bainar jama’a.

Ya caccake su ne kan wasu kalamai nasu da ya bayyana a matsayin munana da ka iya tunzura aikata laifukan yaƙi a Falasɗinu.

Sai dai tuni jami’an diflomasiyya suka bayyana cewa, mawuyaci ne ƙasashen na Ƙungiyar Tarayyar Turai 27 su amince da yawu guda wajen cimma matsayar lafta takunkumai kan ministocin gwamnatin Isra’ila.

Amma ko ba komai, kalaman mista Borrell na nuni da kololuwar fusatar da wasu jami’an ƙungiyar EU suka yi kan yadda ministocin na Isra’ila ke tunzuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)