Yawaitar bola a sassan birnin Rome na Italiya na ci gaba da janyo rikici.
Sakamakon tsananin zafi, mummunan wari da doyi na damun Babban Birnin na Italiya.
Ana aikawa da bolar da ake tarawa a birnin Rome zuwa wajen birnin don zubarwa.
Amma sakamakon yadda babu isasshen wajen zubar da shara a yankin Lazio ya sanya ake samun tsaiko wajen kwashe shara daga unguwanni.