A yammacin jiya Talata ne dai Blinken ya isa birnin Brussels don gudanar da ziyarar ta yini ɗaya, inda zai gana da shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte da babban jami'an diflomasiyya na ƙungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell da wacce za ta gaje shi Kaja Kalas, sai kuma ministan harkokin wajen Ukraine Andriy Sybiga.
Ziyarar ta gaggawa dai ta zo ne bayan nasarar da Trump ya samu na lashe zaɓe, tare da rikicin siyasar Jamus da ya ƙara haifar da fargaba game da makomar taimakawa Ukraine a yaƙin da take yi da mamayar Rasha.
A baya dai Trump ya yi shaguɓe kan dala biliyan 175 da Amurka ta ware don tallafawa Ukraine, tun farkon yaƙin da aka faro a shekarar 2022.
Trump mai shekaru 78, wanda za a rantsar a ranar 20 ga watan Janairun baɗi, ya tattauna da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, bayan nasarar sake zaɓensa da aka yi.
Ya yi iƙirarin kawo ƙarshen yaƙin a rana guda, inda ake gani zai iya yin amfani da hanyar tilasta wa Ukraine, kodayake sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaron ƙasa Mike Waltz, ya ce Trump na iya matsa wa Putin lamba don kawo ƙarshen rikicin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump. AP - Evan VucciJaridar Washington Post ta rawaito cewa zaɓaɓɓen shugaban na Amurka ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da Putin, zancen da tuni fadar Kremlin ta musanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI