Blinken zai gana da ƙasashen larabawa kan rikicin gabas ta tsakiya

Blinken zai gana da ƙasashen larabawa kan rikicin gabas ta tsakiya

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ne ya tabbatar da haka ga manema labarai, ya ce Blinken zai ziyarci birnin London.

A ziyarar da zai kai birnin Blinken zai gana da ministocin wajen ƙasashen larabawa kan rikicin na gabas ta tsakiya a ranar juma’a.

Sakataran harkokin wajen Amurka wanda yake ziyara a ƙasar Saudiyya bayan ziyartar Isra’ela zai je London bayan tattaunawa a Qatar

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurkan bai faɗi ministocin ƙasashe larabawan da za su halaccci wannan taro ba.

Blinken ya ziyarci gabas ta tsakiya har sau 11 cikin sama da shekara guda da barkewar yaƙi a yanki, yana kuma ta kara kaimi wurin ganin an tsagaita wuta a yakin Isra’ila a Gaza tun bayan kashe shugaban kungiyar Hamas Yahya Sinwar.

Har wa yau Blinken na koƙarin amfani da diflomasiyya wurin tsayar da rikicin da ya kunno kai tsakanin Isra’ila da Hezbollah a Lebanon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)