A karo na 11 kenan da Blinken ke ziyartar Gabas ta Tsakiya tun bayan ɓarkewar yaƙi a Gaza shekara guda da ta gabata.
Ziyararsa na zuwa ne a yayin da rikicin na Gaza ya tsallaka zuwa Lebanon, inda ake ci gaba da artabu tsakanin Hezbollah da sojojin Isra'ila.
Tuni dai Blinken ya fara tattaunawa da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kan yadda za a cimma tsagaita musayar wutar.
Ganawar na zuwa ne a yayin da Isra'ila ke ci gaba da nazari kan irin matakin ramuwar gayyar da take shirin ɗauka kan Iran wadda ta yi mata luguden makamai masu linzami a ranar 1 ga watan nan na Oktoba.
Wata majiya ta ce, Blinken zai tattauna da Isra'ila game da shirinta na kai farmaki kuma ana sa ran zai yi duk mai yiwuwa don hana tsanantar yaƙin a Gabas ta Tsakiya.
Gabanin wannan zaman na yau, Amurka ta yi yunƙurin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita musayar wuta a yaƙin na Gaza, amma lamarin ya ci tura.
Bayan ziyararsa a Isra'ila, Blinken zai wuce Jordan a gobe Laraba, inda zai tattauna kan batun samar da kayayyakin jin-ƙai ga al'ummar Zirin Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI