Shugabanni da jami'ai daga kasashe 56 da Biritaniya ta yi wa mulkin mallaka ne ke halartar taron ƙungiyar ta Commaonwealth a wannan makon a kasar da ke tsibirin Pacific.
Gwamnatoci daban-daban da suka gabata a Biritaniya sun yi watsi da duk kiraye-kirayen da aka yi na biyan kasashen da ke buƙata diyya amma Shugabar Hukumar Kula da Al'amuran Yankin Caribbean CARICOM, Hilary Beckles, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa da yiwuwar wannan matsaya ta sauya a ƙarkashin sabuwar gwamnatin jam'iyyar Labor bayan shekaru 14 na mulkin masu ra’ayin ƴan mazan jiya.
Sannan ana sa ran firaministan Burtaniya Keir Starmer da Sarki Charles za su halarci taron na Samoa, inda ake tunanin bullo da wannan bukata a yayin da yake gudana.
Amma mai magana da yawun Starmer ya sake nanata cewa batun biyan diyyar baya cikin shirye-shiryen da za duba a warin taron na Commonwealth.
Duk da cewa batun biyan diyyar ba ya cikin ajandodin taron, mai magana da yawun na Starmer ya kara da cewa za su ci gaba da duba lamuran da wadanda abin ya shafa.
Sannan dukkanin wadanda ke takararar kujerar sakatare janar na ƙungiyar ta Commonwealth sun nuna goyon bayansu akan kudurin na neman diyar bautarwar da aka yi wa magabata a kasashen da Birtaniya ta yiwa mulkin mallaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI