Birtaniya na kusa da samar da allurar riga-kafin Covid-19

Birtaniya na kusa da samar da allurar riga-kafin Covid-19

Allurar vriga-kafin Covid-19 da aka samar a kasar Birtaniya wacce aka yi nasarar gwadawa ya kai wani mataki na biyu mai muhinmanci.

Kamar yadda Imperial College London ta sanar an yi nasara a matakin farko a yayinda aka yi gwajin akan mutane 15 da suka sadukar da kansu, a halin yanzu kuma za'a sake gwajin a mataki na biyu akan wasu wadanda zasu sadaukar da kansu wadanda yawansu zai fi na farkon.

Sabon gwajin da aka fara a wannan makon an yiwa wasu da suka sadaukar da kansu ne su 105 wadanda 'yan shekaru tsakanin 18-75 ne.

An bayyana cewar allurar riga-kafin zata tarwatsa kwayar cutar SARS-CoV-2 dake cikin jikin bil adama.

Shugaban binciken COVIC1 a Imperial College  Katrina Pullock, ta bayyana cewar an yi nasara a gwajin farko amma kawo yanzu ba za'a iya bayyana ko riga-kafin zai iya kare bil adama daga cutar ba.

 


News Source:   www.trt.net.tr