Birrai 43 sun gudu daga cibiyar Alpha Genesis da ke Yemassee, a South Carolina, ranar Laraba, a cewar sanarwar da ‘yan sanda suka fitar.
‘Yan sandan sun ce biran dukkansu mata wadanda nauyinsu bai wuce kilogiram 3 ba.
“Ba su kamu da wata cuta na ko kadan. Ba su da illa kuma ba su da wayo, "in ji shugaban 'yan sandan Yemassee Gregory Alexander, yana mai jaddada cewa babu wani hadari da s uga jama’a.
Alexander ya bayyana cewa, hukumomin gudanarwar Alpha Genesis sun kafa tarko mai amfani da kyamarorin da za su taimaka wajen cafke su cikin sauri, yana mai cewa za a yi amfani da ‘yayan itatuwa da sauran abubuwan da ke jan hankalin birai wajen cafke su.
'Yan sanda sun bukaci mazauna garin, mai yawan jama'a kusan 2,000, da su rufe kofofinsu da tagoginsu, kuma su yi gaggawar bayar da rahoton duk inda suka hango su, tare da gargadin cewa su guji tunkarar birran.
Wannan ba shine farkon tserewar birai daga dakunan da ake killace su ba, domin ko a shekarar 2018, gwamnatin Amurka ta ci tarar Alpha Genesis dala $12,600 bayan da dama daga cikin birran da ke ajiye suka tsere. Akwai kuma wasu da suka tsere a shekarar 2014 da 2016.
Kungiyar Stop Animal Exploitation Now ta aika da wasika zuwa ga ma’aikatar aikin gona ta Amurka inda ta bukaci ta gaggauta aika tawaga ta musamman zuwa cibiyar Alpha Genesus domin gudanar da cikakken bincike kan yadda take tafiyar da ayyukanta.
Michael Budkie, babban darektan kungiyar a cikin wata wasikar ya rubuta cewa, sakaci ne ya haifar da tserewar wadannan birrai har sama da 40, tare da cewa hakan tamkar barazana ce ga rayuwar mazauna kudancin yankin Carolina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI