Bincike ya nuna cewa HDL ce ta kai harin daya kashe cadet din sojoji 26 a Libiya

Bincike ya nuna cewa HDL ce ta kai harin daya kashe cadet din sojoji 26 a Libiya

Wani rihoton BBC ya bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa (HDL) ce ta kai hari da jirgi mara matuki da ya kashe cadet din sojoji 26 da ake hoararwa a makaranatar horar da sojojin kasar Libiya a watan Janairu.

HDL dai ta musanta wannnan zargin da ake yi mata.

Danagane ga rohoton, kamar yadda jaridar Daily Sabah ta rawaito an kaiwa makaranatar horar da sojojin hari ne da makami mai linzami kirar China Blue Arrow 7  da jirgi mara matuki kirar Wing Loong II drone wanda aka harba daga sansanin Al-Khadim dake hannun kulawar HDL a wannan lokacin.

Ana anfani da linzamin da aka harba da jirgi mara matukin ne kawai a China wanda Kazakhstan da HDL suka ta’alaka yin amfani dashi tare da jirgi mara matuki kirar Wing Loong da aka yi a China.

Abu Dhabi dai ta musanata lamarin inda take ikirarin cewa harin da ya kashe cadet din sojoji 26 wadanda mafi yawansu ‘yan kasa da shekaru 20 ne- mayakan cikin gidan kasar Libiya ne suka kai shi.

 

 

 

 

 

 


News Source:   ()