Wani faffadan bincike da aka gudanar ya gano cewar tafiya wajen aiki a kan keke na hana mutuwar dan adam da wuri.
Labaran da aka fitar a shafin yanar gizo na New Atlas na cewa, malaman kimiyya a Jami'o'in Imperial College London da Cambridge sun gudanar da nazari kan bayanan mutane dubu 300 da suke zuwa aiki su dawo a tsakanin shekarun 1991 da 2016.
Sakamakon binciken da aka gudanar wanda aka buga a mujallar "The Lancet Planetary Health" ya nuna cewa zuwa wajen aiki a kan keke na rage hatsarin mutuwa da wuri da kaso 20 cikin dari, sannan yana rage hatsarin kamuwa da cutar hanta da kaso 24 cikin dari.
A bangaren masu ciwon daji kuma masu zuwa aiki a kan keke ba sa fuskantar matsalar kamuwa da cutar da kaso 16 cikin dari.