Bincike: Kwayoyin cuta zasu iya shekaru a sararin samaniyya

Bincike: Kwayoyin cuta zasu iya shekaru a sararin samaniyya

Binciken da masanan kimiyya da fasahar tashar sararin samaniya ta kasa da kasa (ISS) a Japan suka gudanar ya nuna cewa kwayoyin cuta na iya rayuwa a sararin samaniya na tsawon shekaru.

Masanan sun bayyana cewa wannan binciken ya tabbatar da cewa kwayoyin cutar bakteriya ka iya yawo a cikn duniya daban daban dake cikin sararin samaniyya.

Masana kimiyya da fasahan a kasar Japan sun gudanar da wannan binciken ne mai suna 'Tanpopo' a cikin shekaru uku.

A gwajin da suka yi tare da wani nau'in kwatyar cuta mai suna ‘Deinococcus radiodurans’ sun gano cewa kwayar cutar zata iya kasance har na tsawon shekaru uku a sararin samaniyya.

Dangane ga sakamakon binciken kwayoyin cutan zasu iya tafiya a tsakanin ire-iren duniyar dake cikin sararin samaniyya kamar su duniyar mutane da duniyar Mars.

 


News Source:   ()