Hukumar kare hakkokin masu siyar kayayyaki ta kasar Faransa wato UFX-Que Choisir ta bayyana cewa sinadiran da ake zanen tattoos da su na dauke da guba masu cutarwa.
Jaridar Le Monde ce ta rawaito cewa kasancewar sinadiran tattoos din nada carcinogenic da neurotoxic a cikinsu zasu iya cutarwa inda ta yi jan kunne game da hakan.
UFC-Que Choisir ta kaddamar da bincike inda ta yi bincike akan tawada 20 daga cikin wadanda aka fi amfani dasu wajen zanen tattoos a duniya inda ta gano cewa biyar daga cikinsu ne kawai suka cancanta.
Binciken ya tabbatar da cewa akwai sinadarai masu guba kwarai da gaske a cikin mafi yawan dawadun da ake amfani dasu wajen yin zanen tattoo wadanda ke cutarwa sosai ga bil adama.
Kungiyar ta yi kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace ganin irin yadda sinadaran da ake amfani dasu suna cutarwa kwarai da gaske.