Bincike: China bata sanar da duniya bulluwar Covid-19 cikin lokaci ba

Bincike: China bata sanar da duniya bulluwar Covid-19 cikin lokaci ba

Hukumar leken asirin kasar Amurka ta yi ikirarin cewa hukumomin Wuham inda kwayar cutar Corona ta samo asali sun boyewa gwamnatin Beijin faruwar lamarin na tsawon makonni.

Kamar kafar yada labaran CNN ta rawaito hukumar lekan asirin Amurka ta yi ikirarin cewa jami'an Wuhan basu bayyanawa gwamnatin China bulluwar cutar Covid-19 cikin lokaci ba.

Bugu da kari rahoton hukumar leken asirin ta kara da cewa bayan gwamnatin China ta samu labarin bulluewar cuta taki sanar da sauran kasashen duniya cikin lokaci.

Jami'an dake magana da CNN ya tabbatar da cewa a yayinda hukumar ke cigaba da bincike akan bulluwar kwayar cutar Covid-19 ya jaddadda cewa ko shakka babu hukumominn China sun boye bulluwar cutar na wasu ;lokutta gabanin su sanarwa duniya.

 


News Source:   ()