Wani binciken jin ra'ayin al'umma ya bayyana cewa Amurka na cikin yanayin kunci da rashin dadi da basu taba samun kansu a ciki ba a cikin shekaru 50 da suka gabata.
Cibiyar Binciken Ra'ayoyin Mutane dake Jami'ar Chicago ce ta gudanar da binciken jin ra'ayin al'umma wanda mutum dubu 2 da dari 279 suka halarta a tsakanin ranakun 21-29 ga watan Mayu. Dangane ga tambayar da aka yi musuko suna cikin farin ciki an samu raguwar wadanda suka amsa ehh daga kaso 31 zuwa kaso 14 cikin dari idan aka kwatanta dana shekarar bara.
Wadanda suka kasance sun jin kansu cikin halin kadaici kuwa ya karu daga kaso 23 zuwa kaso 50 cikin dari.
Da ngane ga binciken Amurkawa na cikin halin rashin farin cikin da basu taba samun kansu a ciki ba a cikin shekaru 50 da suka gabata.
Amurkawa kaso 58 cikin dari na ganin cewa al'umman da zasu gabcesu zasu fi kasancewa cikin kyawawan hali.