Bikin ranar Tarayyar Turai a Turkiyya

Bikin ranar Tarayyar Turai a Turkiyya

A yau 9 ga watan Mayu ne ma'aikatar Tarayyar Nahiyar Turai dake Turkiyya take gudanar da bukukuwan ranar tarayyar da shirye-shirye iri daban-daban.

A bukukuwan da mawakar Antakya zasu shirye wakillan addinai uku zasu gabatar da kide kide, wakokin kade-kade da raye-rayen jama'a.

Zasu baiwa duniya sakon haƙuri, haɗin kai da juriya.

Bikin da zai dauki kusan mintuna 30 za'a gudanar dashi da misalin karfe 21.00 agogon Turkiyya kuma za'a yada su a shafukan sadar da zumunta ta ma'aikatar harkokin nahiyar Turai ta kasar Turkiyya.

Mataimakin ministan harkokin waje Faruk Kaymakcı ya bayyana cewa Turkiyya da Nahiyar Turai sun kara kusanatar juna a yayinda duniya ke kalubalntar annoba.

Wannan bikin ranar Tarayyar Turai zai kasance sako ga kasashen Turai da kuma duniya baki daya.

 


News Source:   www.trt.net.tr