Bidiyon zanga-zangar kisan George Floyd a Amurka

Bidiyon zanga-zangar kisan George Floyd a Amurka

Amurkawa sun tshi tsaye domin kalubalantar ukubar 'yan sanda da ya yi sanadiyar rauwar wani bakar fata mai suna George Floyd a ranar Talata.

Zanga-zangar da Amurkawan ke yi domin kalubalantar ukubar 'yan sanda akan bakaken fata a kasar lamarin dake haifar da rasa rayukansu na cigaba da karuwa.

Hakan ya sanya karfafa tsaro a jahoji 8 da kuma kafa dokar ta baci na hana fita waje da dare a birane 25 dake a wasu jahohin kasar 16.

A hukumar 'yan sandan Minneapolis dinbin al'umma sun taru suna kira da abiwa George Floyd hakkinsa. Sun dai kasance dauke da allunan dake kira da hakan.

Bayan fara wannan zanga-zangar 'yan sanda sun dinga amfani da barkonon tsuhuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar haka kuma an kara yawan jami'an tsaro a garin daga 500 zuwa dubu 10.

Shugaba Donald Trump, a nasa bangaren, ya mai da martani tare da furucin cewa "sojoji a shirye suke don dakile abubuwan da ke faruwa".

Trump ya bayyana cewa masu zanga-zangar basu kasance ba face masu nuna rashin girmamawa ga Floyd. Inda ya kara da cewa,

"Mutuwar George Floyd a kan titin Minnesota babban bala'i ne. Wannan bai kamata ya faru ba. Wannan abin tsoro ne ga. Amurka bata taba kasancewa tana fusata 'yan kasarata ba"

A shekaran jiya Trump ya bayyana cewa wadanda suka bayyana a gaban fadar White House domin gudanar da zanga-zanga idan suka wuce iya zasu hadu da karnuka.

Duk da haka daruruwan masu zanga-zangar sun sake taruwa a gaban fadar gwamnatin kasar inda suka kwashi artabu da jami'an tsaro.

Donald Trump ya nemi magoya bayan sa da su nuna masa goyan baya a gaban Fadar White House, inda ya kara da cewa,

"Kashi 80 cikin 100 na masu zanga-zanga a Minneapolis sun fito ne daga wajen jihar." Ya yi zargin cewa wadannan mutane suna cutar da kananan kamfanoni, gidaje, kadarorin jama'a.

A maimakon Donald Trump ya dauki matakan kwantar da tarzoma ya rinka sharhin sabanin haka inda yake godewa magajin garuruwa da suka dauka tsararra matakai akan tarzomar tare da yi musu godiya akan kamen da suka bayar da umarnin aka yi.

Haka kuma ma'aikatar tsaropn Pentagon ta bayyyana cewa a shirye take ta bayar da gudunmowa jahohin da tarzomar ke ci gaba da faruwa.

George Floyd mai shekaru 46 ya mutu ne bayan wani dan sanda ya shake wuyarsa har ya kasa numfashi a yayin kamashi da zargin yin damfara.

 


News Source:   www.trt.net.tr