Shugaban kasar Amurka Joe Biden zai fara ziyarar kasashen waje ta farko zuwa Ingila da Belgium a watan Yuni.
Kakakin Fadar White House Jen Psaki ta bayyana a rubutacciyar sanarwa cewa Biden, wanda ya hau mulki a ranar 20 ga watan Janairu, zai halarci taron shugabannin G7 da za a gudanar a Cornwall, Ingila a tsakanin 11-13 ga Yuni, a matsayin wani bangare na ziyarar sa ta farko zuwa kasashen waje.
Psaki ta kara da cewa,
"A nan, Biden zai tabo batun sadaukar da kai da yake yi daga bangarori daban-daban, manufofin Amurka kan fifikon kiwon lafiyar jama'a, da alkawurran da ta dauka na farfado da tattalin arziki, da yaki da sauyin yanayi. Hakan kuma zai tabo batun hadin kai da kuma martaba juna a tsakanin manyan kasashen dimokuradiyya."
Psaki ta lura cewa Biden zai yi ganawar bangarorin biyu tare da shugabannin G7, ciki har da Firaiministan Biritaniya Boris Johnson.
Da take bayyana cewa Biden zai je Brussels, babban birnin Belgium domin taron NATO a ranar 14 ga watan Yuni, bayan Biritaniya, Psaki ta kara da cewa,
"Biden zai sake jaddada aniyar Amurka ga kungiyar tsaro ta NATO, tsaro a yankin da kuma ayyukan hadin gwiwa na tsaro."
Psaki ta bayyana cewa Biden zai kuma halarci taron kolin Amurka da Tarayyar Turai da za a yi a Brussels tare da yin tattaunawa tskanin kasashe biyu.