Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa, suna sa ran a cikin awanni 24 da zuwa 36 za a sake kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul Babban Birnin Afganistan.
Bayan Biden ya karbi bayanai daga jami'an tsronkasa, ya yi jawabi kan halin da ake ciki a Afganistan.
Biden ya shaida cewa hari da jirgin sama mara matuki da Amurka ta kai 'yan ta'addar Daesh-Horasan bayan sun kai harin bam da ya kashe mutane da dama a Kabul ba shi ne na karshe ba.
Ya ce, "Yanayin da ake ciki na da matukar hatsari. Kuma akwai barazanar yiwuwar kai harin ta'addanci a filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul. An fada min cewa a cikin awanni 24 zuwa 36 akwai yiwuwar a sake kai hari a filin tashi da saukar jiragen saman na Kabul."
Biden ya ci gaba da cewa, za a ci gaba da mayar da martani ga duk wani hari na ta'addanci da za a kai inda ya ce,
"Na fadi cewa za mu bi bayan 'yan ta'addar da suka kaiwa sojojinmu da fararen hula hari, kuma mun cimmusu. Za mu kama dukkan masu hannu a wannan hari kuma za su dandana kusarsu."