Biden ya zargi Natenyahu da jan kafa a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Gan-Gan

Biden ya zargi Natenyahu da jan kafa a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Gan-Gan

Da yake jawabi shugaba Biden ya ce dukannin alamu sun nuna cewa Natenyahu ba’a shirye yake ya kawo ƙarshen yaƙin da ake tafkawa ba, abinda ke ci gaba da laƙume rayukan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Biden ya ce batun cimma wannan yarjejeniya abu ne mai matuƙar muhimmanci da ya kamata ayi shi cikin gaggawa, don haka akwai takaici ƙwarai yadda Natenyahu ke jan ƙafa kawai don biyan wata buƙata ta kansa.

Bayanan na Biden na zuwa ne yayin da zanga-zanga ke ci gaba da gudana a birnin Tel Aviv da sauran biranen Isra’ila don yunƙurin tilastawa gwamnati Natenyahu rattaba hannu kan yarjejeniyar don ƙwato sauran mutanen da Hamas ke garkuwa da su.

Har yanzu jama’a na nan kan titunan Isra’ila duk da umarnin kotun ma’aikata na buƙatar ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki da kuma zanga-zangar da ta kira duk kan batu guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)