Shugaban Joe Biden ya bayyana jinkirta kai ziyarar ce bayan samun cikakkun bayanai daga ƙwararru da ke tabbatar da cewa guguwar za ta iya kasancewa mafi muni da Amurka ta taɓa fuskanta a cikin shekara 100 na baya-bayan nan, inda ya buƙaci da su gaggauta cewa sun fice daga gidajensu domin fakewa a tundun-mun-tsira.
Masu hasashe sun ce a lokacin da guguwar Milton ke isa jihar Florida a wannan laraba, ƙarfi da kuma ɓarnar da za su iya zarta waɗanda aka taba gani a sauran guguwa da ambaliyar da afka wa ƙasar cikin shekaru ɗari da suka gabata.
Gwamnan jihar Florida Ron DeSantis, ya ce suna sa ido sosai a game da yadda guguwar da kuma ruwan sama ke kaɗawa, duk da yake Hukumar Hasashen Yanayi ta ƙasa (NHC) ta ce ƙarfin kaɗawar zai ragu daga maki 5 zuwa maki 4 a wannan laraba.
Ita dai wannan guguwa tana tashi ne daga yankin kudu maso yammaci zuwa arewa maso gabashin Amurka, amma ba za a iya tantance irin ɓarnar da za ta haddasa ba har sai zuwa tsakiyar daren laraba zuwa wayewar garin safiyar alhamis.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan makamanciyarta mai suna Helene da ta afka wa yankin, yayin da ake tsakiyar yaƙin neman zaɓen neman shugabancin ƙasa da za a yi cikin watan nuwamba mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI