
Matakin na zuwa ne watanni biyu gabanin Biden ɗin ya miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaba Donald Trump.
Wani babban jami’in gwamnatin Amruka ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, makaman da Biden ya ba wa Volodymyr Zelenskyy umarnin yin amfani dasu akan Rasha, masu cin zangon kilomita 300 ne.
Kafin matakin na Amurka dai an yi ta samun saɓanin ra’ayi tsakanin shugabanin ƙungiyar Tarayyar Turai game da bai wa Ukraine damar amfani da makamai masu cin dogon zango da suke bata akan Rasha.
Sai dai duk da cewar ƙasar ta Ukraine ta daɗe tana neman a bata wannan dama, wasu jaridu sun bayyana cewar a ranar Lahadin da ta gabata, shugaba Volodymyr Zelenskyy ya nuna ɗari-ɗari a gameda iƙirarin na gwamnatin Amruka, ya na mai cewa irin wannan matakin ba da fatar baka ake ɗaukarsa ba, ya dace ne a ga makaman a hannu da kuma aiwatarwa a zahiri.
Jaridar New York Times da ake wallafa ta a Amruka, ta ce ɗage haramcin da fadar White House ta yi wa Ukraine na amfani da makaman ta cikin Rasha, na a matsayin martani kan matakin Korea ta Arewa na aikewa da dakaru dubu 10 zuwa Rasha domin taimaka mata a yaƙin da take fafatawa da Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI